28 Agusta 2020 - 13:32
An Sake Zaben Adesina A Karo Na Biyu

An sake zaben Akinwunmi Adesina a matsayin shugaban bankin ci gaban Afrika na AfDB.

ABNA24 : Mista Akinwunmi, zai jagoranci bankin na karin wasu shekara biyar a wa’adi na biyu.

Tsohon ministan aikin gona na Najeriya ya dai lashe zaben ne babu abokin hammaya.

A kwanakin baya ne wani kwamiti na musamman da aka kafa ya wanke Adesina, daga zargin nuna bambamci tare da fifita ‘yan Najeriya wajen bayar da aiki da kuma kwangiloli a bankin na AfDB.

A jawabinsa na soma aiki a karo na biyu, Mista Adesina ya ce zai mayar da hankali kan yin aiki tukuru domin ci gaban nahiyar Afrika ba tare da nuna son zuciya ba.

342/